A ranar Talata da ta gabata ne Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta zartar da kudirin dokar hakar ma’adanai da ya tanadi tsari da kuma ba da izinin filaye da yarjejeniyar da al’umma ke yi ga masu hakar ma’adanai ta al’umma.
Kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa Dokta Danladi Jatau wanda ya sanar da amincewa da kudirin a zaman majalisar ya ce dokar za ta bunkasa ayyukan hakar ma’adinai.
Jatau ya ce idan aka amince da dokar za ta magance kalubalen hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a jihar.
Shugaban majalisar ya yi karin haske kan wasu bangarori na dokar da suka hada da hukuncin keta ko rashin bin duk wani tanadi na dokar.
“Don hakar ma’adinanh hukumomi Da kamfanoni za su biya tarar Naira miliyan 10 ko mafi karancin shekaru 2 da kuma hukuncin daurin shekaru 5 a gidan yari.
“Duk wani mutum ko mutane zai su biya tarar Naira miliyan 5 ko mafi karancin shekaru 2 da kuma hukuncin daurin shekaru 5 a gidan yari.
Shugaban majalisar ya kuma ce, kudirin dokar ya ba da umarnin samar da Asusun raya Al’umma (CDF) don inganta rayuwar al’ummomin da ke hakar ma’adanai ta hanyar samar da ayyukan more rayuwa da ayyukan jin kai.
“Kamfanonin hakar ma’adinai za su ba da gudummawar kashi 5 cikin 100 na kudaden shigarsu na shekara ga CDF. Kashi 50 na kudaden da ke cikin asusun CDF za a yi amfani da su ne don biyan kudi ga al’ummar da ke amfana yayin da kashi 50 cikin 100 za a kai su ga samar da ayyukan yi,” in ji shi.
Kakakin majalisar ya umurci magatakardar majalisar da ya gabatar da kwafin kudirin doka mai tsafta don amincewar gwamnan.
Tun da farko Suleiman Azara shugaban masu rinjaye na majalisar ya gabatar da kudirin dokar a karatu na uku; Luka Zhekaba shugaban marasa rinjaye ya goyi bayan matakin.
NaN/Aisha.Yahaya, Lagos